SHUGABAN NAJERIYA, BOLA AHMED TINUBU YA TAYA MAI DAKINSA, OLUREMI MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWARTA INDA TAKE CIKA SHEKARA 66 A DUNIYA.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya mai ɗakinsa, Oluremi murnar zagayowar ranar haihuwarta inda take cika shekara 66 a duniya.
Ya bayyana ta a matsayin babbar aminiyarsa kuma abokiyar shawara.
Cikin wani saƙon taya murna mai ratsa zuciya kuma cike da kalaman soyayya, Shugaba Tinubu ya jinjinawa Oluremi bisa kasancewa tare da shi da haƙuri da kuma ƙarfafa masa gwiwa.
A cewarsa, nauyin da ke kan wuyansa, a mafi yawan lokuta suna sauka ne a kafaɗun Oluremi yayin da take saurin fahimtar abubuwan da ke zuciyarsa ko da bai furta su ba.
Tinubu ya ce "a yanayi na ƙalubale, na rashin sanin abin da gobe za ta haifar, kin kasance tare da ni kuma muna addu'a tare."
Ya bayyana Oluremi a matsayin wadda ta fahimce shi sosai kuma sau da yawa tana saurin gane yana buƙatar shawara kafin ma na nema.
Tinubu ya kuma yaba da sadaukarwarta ga iyalanta inda ya ce ƴaƴansu da jikokinsu sun taso ƙarƙashin inuwar addu'ointa kuma sun gaji kyawawan ɗabi'unta.

Comments
Post a Comment
Share your thoughts here. We welcome your comments and suggestions. Thank you for visiting Lamielsid News.”