SHUGABAN IRAN ZAI JE BIRNIN NEW YORK A RANAR TALAKA DOMIN HALARTAR BABBAN TARON MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA.

 Shugaban Iran zai je birnin New York a ranar Talata domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.



Sa’o’i kaɗan da suka gabata, Donald Trump ya ce a shirye yake ya gana da Masoud Pezeshkian, yana mai gargadin cewa idan ba a cimma yarjejeniya ba, Iran na iya fuskantar durƙushewar tattalin arzikinta ko kuma gagarumar barna.


Ziyarar Masoud Pezeshkian zuwa shalkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke New York ta janyo ce-ce-ku-ce.


Wasu jiga-jigan masu ra’ayin mazan jiya, da ma wasu ’yan siyasa masu fafutuka da ke da alaƙa da wannan ɓangare ko kuma masu rajin kawo sauyi, sun nuna shakku kan ziyarar.


Wasu masu sukar ziyarar sun ce, tun da aka ƙi ba wa tawagar kafafen watsa labarai ta shugaban Iran biza, ba zai yiwu a bayar da sahihan rahotannin ziyararsa ba.


Bugu da ƙari, wasu masu ra’ayin mazan jiya na ganin cewa, la’akari da halin da ake ciki na yaƙi, halartar Iran na iya zama alamar cewa a shirye take ta shiga tattaunawa, lamarin da ka iya sanya ƙasar cikin raunin diflomasiyya.


Sun kuma yi imanin cewa Fadar White House na iya kallon ziyarar a matsayin wani mataki na shirye-shiryen neman Iran ta yi rangwame.


Sai dai masu goyon bayan gwamnati sun ce rashin halartar Iran babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya zai amfani Amurka ne, kuma yana da muhimmanci a ci gaba da samar da damar diflomasiyya.

Comments