From the first day of the Hood to today, a lot has happened.
Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi kakkausan martani ga kalaman Trump a jawabin da ya gabatar a taron UNGA da ke gudana a birnin New York na Amurka.
Mista Pezeshkian ya ce ƙasarsa ta kasance "wadda ke shan wahalar ayyukan ta'addanci", yana mai mayar da martani ga kiran da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wa Iraniyawa da ya bayyana su a matsayin "'yan ta'adda".
Pezeshkian ya zargi Amurka da kai hare-hare kan shugabanninsu da masana kimiyya tare da cibiyoyin ilimi da cibiyoyin lafiya da makarantu da asibitoci da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Ya ce an kashe yara marasa laifi a makarantu sakamakon hare-haren.
Shugaban na Iran ya ce asar na kare kanta ne daga hare-haren da ake kai mata.
Comments
Post a Comment
Share your thoughts here. We welcome your comments and suggestions. Thank you for visiting Lamielsid News.”