Featured post

Kylian Mbappé yana cikin ƴan wasa 30 da aka zaɓa domin takarar Ballon d'Or ta 2026.

Image
   Kylian Mbappé yana cikin ƴan wasa 30 da aka zaɓa domin takarar Ballon d'Or ta 2026, amma tambayar da ke tasowa ita ce: Shin ɗan wasan Real Madrid zai iya lashe babbar kyautar ɗan ƙwallo mafi fice a duniya a bana duk da cewa bai ɗauki babban kofi ba a kakar 2025/26? Dokokin Ballon d'Or ba su ce dole sai ɗan wasa ya lashe kofi ba a kakar kafin ya samu damar lashe kyautar. A tsarin 2026, an bayyana ma'auni uku da da za a yi amfani da su wajen tantance ɗan wasa da zai zama gwarzon bana Waɗanne abubuwa ake dubawa. France Football mai gudanar da bikin ta bayyana cewa ana duba abubuwa uku, cikin waɗan nan tsari don zaƙulo zakara: 1. Ƙwazon ɗan wasa da tasirinsa a fili Wannan shi ne ma'aunin farko. Ana duba yadda ɗan wasa ya taka leda da tasirinsa a wasanni da ya buga a kakar da cin ƙwallaye da kuma yadda ya kasance mai muhimmanci ga ƙungiyarsa da kuma ƙasarsa. 2. Gudunmuwa a ƙungiya da kofunan da aka lashe da shi Wannan shi ne ma'auni na biyu. Don haka lashe kofuna yana...

Shugaban Ƙasar Iran, Mas’oud Pezeshkian, ya ɗaga hoton marigayi Ayatollah Ali Khamenei tare da jakar

   


Jiya a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Shugaban Ƙasar Iran, Mas’oud Pezeshkian, ya ɗaga hoton marigayi Ayatollah Ali Khamenei tare da jakar makaranta domin tunawa da yaran makarantar Minab da suka rasa rayukansu a harin da aka kai makarantar.


Rahotanni sun ce harin ya kashe ɗalibai da ma’aikatan makarantar da dama. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce akwai hujjojin da ke nuna cewa Amurka na da alhakin harin, yayin da Amurka ba ta amince da hakan a matsayin tabbataccen alhaki ba. 


Lamarin ya sake janyo ce-ce-ku-ce kan kare fararen hula da makarantu a lokacin yaƙi.

Comments

Popular posts from this blog

BAUCHI STATE HAS LAUNCHED RECRUITMENT EXERCISES OFFERING OPPORTUNITIES ACROSS VARIOUS SECTORS, INCLUDING EDUCATION, HEALTHCARE, ENGINEERING, AND ADMINISTRATION 2025?

THE GOLDEN STAR IN THE SKY THANK YOU SO MUCH GOOD BLESS YOU?

BAUCHI STATE UNIVERSITY GADAU OR SAZUG ON FIRE INCIDENT?