From the first day of the Hood to today, a lot has happened.
Lokacin da Shugaban China Xi Jinping zai isa birnin Washington ranar Laraba, zai kasance karon farko cikin shekaru 11 da ya kai ziyarar aiki ta ƙasa a Amurka.
Sai dai dangantakarsa da Amurka ta fara tun kafin ya zama ɗaya daga cikin shugabannin China mafiya ƙarfi cikin shekaru da dama.
Shekaru 40 da suka gabata, Xi Jinping wani ƙaramin jami'in gwamnati ne a matakin ƙaramar hukuma a arewacin China, lokacin da ya je tsakiyar Amurka domin duba yadda ake gudanar da ayyukan noma a wurin.
Ya shafe wasu kwanaki a jihar Iowa, inda ya koyi yadda ake noma, ya ziyarci gonaki, sannan ya sauka a gidan wani iyali a wani yanki da ke kusa da birni
Comments
Post a Comment
Share your thoughts here. We welcome your comments and suggestions. Thank you for visiting Lamielsid News.”